• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babu Wata Kasa Da Za Ta Ce ”Ita Kadai Ta Isa Gayya”

by CGTN Hausa and Sulaiman
12 months ago
Kasa

An yi zama na II na taron kungiyar G20 karo na 19 a jiya Litinin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taken ”Hada Hannu Domin Tafiyar da Tsarin Tattalin Arzikin Duniya Bisa Adalci da Daidaito”. 

A ra’ayina, wannan jawabi ya gabatar da shawarwari da hanya mai sauki ta shawo kan matsalolin tattalin arziki da duniya ke fama da su, har ma da hanyoyin da kasashe za su iya hada hannu domin taimakon juna.

  • Sin Da Afirka Na Da Buri Daya A Wajen Taron G20
  • Shugaba Xi Jinping Ya Ce Kasar Sin Da Birtaniya Na Da Dimbin Sararin Yin Hadin Gwiwa

Daga cikin kalaman shugaba Xi, akwai wadanda suka fi jan hankalina, inda yake cewa, ya kamata a yi adawa da kariyar cinikayya da ra’ayin bangare daya da sanya yarjejeniyar saukaka zuba jari domin samun ci gaba, cikin tsarin dokokin WTO.

LABARAI MASU NASABA

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Zan iya cewa, cikin wadannan kalamai kalilan, shugaban ya gabatar da mafita mafi sauki ga matsalolin duniya. Idan muka dauki batun kariyar cinikayya da zartar da ra’ayin bangare guda da wasu kasashen duniya ke ganin su ne mafita gare su, mun riga mun ga yadda hakan bai amfanawa kowannne bangare da komai ba. Ci gaban wata kasa, dama ce ga sauran kasashen duniya maimakon barazana ko kalubale. Mun riga mun gane cewa, babu wata kasa da za ta iya cewa za ta raba gari da wata, domin makomar kasashen na hade da juna. Idan wata na fama da talauci ko matsaloli, to wadannan matsaloli na iya bazuwa ga sauran, haka ma idan tana cikin wadata da kwanciyar hankali. Idan muka dauki Sin a matsayin misali, muhimmiyar rawar da take takawa wajen samarwa duniya damarmaki da dimbin gudunmuwarta ga ci gaban tattalin arzikin duniya, abu ne da ba zai misaltu ba, don haka, babu wata kasa da za ta ce ta yanke mu’amala da ita ko kuma ta bugi kirjin cewa ita kadai (kasar) ta isa gayya.

Idan har ba neman fifiko ko mulkin danniya ba, to mene ne dalilin wariya ko kariyar cinikayya tsakanin kasashe bayan mafita ita ce hada hannu tsakaninsu domin cin moriyar juna? A wannan zamani da ake ciki, ba zai yuwu duniya ta ci gaba da kasancewa karkashin ikon wata kasa daya ko wasu kasashe kalilan ba, dole ne irin wadannan kasashe su zubar da girman kai su hada kai da sauran takwarorinsu domin ceto duniya daga fadawa mummunan yanayi. (Fa’iza Musatapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin
Daga Birnin Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong
Daga Birnin Sin

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE
Daga Birnin Sin

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

November 8, 2025
Next Post
Kwalara Ta Yi Ajalin Mutane 25 A Sakkwato

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

November 8, 2025
Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

November 8, 2025
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Yadda Ake Miyar Margi

Yadda Ake Miyar Margi

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

November 8, 2025
Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.