Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, abokin hadin gwiwar kafar watsa labarai na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ne na dogon lokaci, shi ya sa ma’aikatansa sama da 2000 za su gudanar da aikin watsa labarai game da gasar wasannin Olympics da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa a shekara mai zuwa.
Kwanan baya shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach ya yi tsokaci yayin da ya zanta da wakiliyar CMG cewa, “Muna farin ciki matuka da gudanar da hadin gwiwa da CMG, saboda da mun ga nasarorin da ya samu yayin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da aka shirya a birnin Beijing a shekarar 2022 da ta gabata.
Mun ga fasahohin zamanin da ya yi amfani da su yayin aiki, haka kuma mun lura cewa, ‘yan kallo Sinawa suna son kallon shirye-shiryen wasannin da babban gidan rediyo da talibijin din ya watsa matuka.” (Mai fassarawa: Jamila)