Hukumar Karbar Koke-Koke da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta cafke ma’aikata takwas na kamfanin samar samar da kayan noma (KASCO) kan zargin almundahanar sama da Naira biliyan 4.3 a shekara guda.
Kazalika, hukumar ta kwace kadarori da suka hada har da rumbun adana kayan noma guda takwas da ke dauke da motoci, tiraktoci, dubban buhunan taki, waken suya, siminti, dawa, da wasu da dama da ake zargin an saye su da lalitar gwamnati.
- ’Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban JIBWIS, Sun Sace Mutane 50 A Kaduna
- Yau Real Madrid Da Barcelona Za Su Barje Gumi
Shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana haka a ranar Asabar.
Ya ce kadarorin da aka kwato a karamar hukumar Kubmotso, bincike ya nuna cewa an yi amfani da wasu kamfanoni wajen yin da zambar.
“Wannan kamfanin Association of Compassionate Friends an yi masa rijista a 2019 da manufar taimakawa da rage barace-barace ga yara, shi kuma kamfanin Limestone Processing Links an mawa rijista ya samu miliyan 480.”
Ya ce kadarar an kwace ta tare da mika ta ga ‘yansanda bayan samun umarni daga kotu.
A umarnin kotun, akwai sunan manajan kamfanin KASCO, Bala Inuwa Muhammad, da aka ce ba a san inda yake ba a halin yanzu a matsayin wanda ake zargi na farko a cikin mutum tara da suka hada da Najib Muhammad, Abdullahi Ibrahim, Aminu Sadiq, Umar Alhassan, Surajo Lawal, Safiyanu Tsakuwa, Nura Yusuf da Aminu Fagge Lawal.
Wata majiya ta ce, kamfanin KASCO daga ranar 19 ga watan Agustan, 2022 zuwa 3 ga Afrilun 2023, ya biya kamfanin Association of Compassionate Friends kudi har naira biliyan 3.2 a lokuta daban-daban har 12 da kuma miliyan N480 da aka biya kamfanin Limestone Processing Links a karo biyu.
“Mun tabbatar an biya miliyan 20, miliyan 30 da miliyan 78.6 zuwa asusun masu zaman kansu da wata gidauniya daya,” cewar masu bincike.