Bankin Duniya ya takatar da Kamfanonin Nijeriya biyu Biba Atlantic Limited da Technology House Limited har na zuwa wata daya daga yin dukkanin yin wata kwangila.
Bankin ya dauki wannan matakin ne, saboda aikata badakal da aikata cin hanci da rashawa a karkashin aiki na kasa na NSSNP, na tura kudaden jin kai ga marasa karfi.
- Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba
- Gwamnatin Katsina Ta Fitar Da Naira Miliyan Dubu 50 Domin Samar Da Ruwan Sha
A cikin sanarwar da Bankin na Duniya da ke da shalkwata a birnin Washington ya fitar a ranar Alhamis, dakatarwar ta kuma shafi Shugaban Kamfanin Norman Bwuruk Didam.
Sanarwar ta kara da cewa, wani bincike ya nuna cewa, rassan Bankin na Duniya da ke yakar cin hanci da rashawa a 2018 ya duba wasu tsare-tsaren bayar da kwangiloli ne, suka bankado da wannan badakalar da ta shafi Kamfanonin na Biba Atlantic da na Technology House da kuma Didam.
A cewar sanarwar, a bisa ka’ida Bankin na Duniya yak an tallata cewa, Kamfanoni da kuma daidaikun mutane da ke bukatar neman kwangila a gun bankin, musamman wadanda suka cancanta, za su iya shiga cikin jeren masu nema, domin shii kuma Bankin, ya bayar da kudaden.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Kamfanin na Biba Atlantic da Didam, sun sana son ra’ayin a cikin wasikar su ta samun umarni tare da samun bayanan sirri, daga gun ma’aikata, ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ya ba su dama tabka badakala da aikata cin hanci da rasahawa.
Kazakla, sanarwar ta bayyana cewa, daga cikin yarjejeniyar, kamfanonin na Biba Atlantic Limited da Technology House Limited da kuma Didam, sun amsa laifinsu da kuma zubar da kimarsu.
Sanarwar ta bayyana cewa, wasu daga cikin abubuwan da ake bukatar Kamfanonin da kuma Didam da ake son su cika sharudda dole ne su bi ka’idar samun haro, kuma wajbi ne, su karfafa kimar bin ka’idar tsare-tsaren su.
Bugu da kari, dole ne wanzar ka’idar samun haro na shirye-shiryen su dai da da ka’idojin da Bankin Duniya, ya gindaya.