Kwamitin majalisar wakilai mai kula da kararrakin jama’a ya bayar da umurnin sammacin kama gwamnan babban bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, kan kin gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi kan harkokin man fetur.
Kwamitin ya kuma bayar da umurnin kama Akanta Janar na Tarayya, Oluwatoyin Madein da wasu mutane 17.
- Kisan Masu Mauludi A Kaduna Abun Takaici Ne – Bukola Saraki
- ‘Yansandan Sun Kama Masu Laifi 130 A Watan Nuwamba A Katsina
Daga cikin mutane 17 da za a yi sammaci har da shugabannin Hukumar Kula da Zuba Jari ta Man Fetur (NAPIMS), kamfanin Ethiop Eastern Exploration and Production Company Ltd, da Western Africa Exploration and Production.
Sauran su ne, shugabannin Alteo Eastern E&P Co. Ltd., First Exploration & Production Ltd., The Md, First E&P Oml 8385 Jv, Heirs Holdings Oil da Mobil Producing Nigeria Unlimited (Mpnu).
Acikin jerin kamfanonin akwai manyan kamfanonin hakar danyen man fetur, Shell Petroleum Development Company (SPDC), Total Exploration & Producing Nig (TEPN), Nigeria Agip Oil Company (NAOC), Pan Ocean Oil Nig, Ltd, Newcross E&P Ltd da Frontier Oil Ltd.
An cimma matsayar ne a zaman binciken kwamitin domin duba karar da wani Fidelis Uzowanem ya shigar a ranar Talata.
Shugaban kwamitin majalisar, Hon. Michael Etaba (APC, Cross River), ya ce Cardoso da sauran wadanda ake tuhuma sun ki mutunta gayyatar da kwamitin majalisar ya yi musu.
Saboda haka, wani mamba a kwamitin, Fred Agbedi (PDP, Bayelsa), ya gabatar da bukatar bayar da sammacin kama duk wadanda sukaki mutunta gayyatar kwamitin.
Abedi ya ce, yana bukatar a gabatar masa da wadanda sukaki amsa gayyatar a gaban kwamitin a ranar 14 ga watan Disamba.
Kwamitin ya amince da kudirin, inda ya umarci Sufeto Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, da ya tabbatar an sammaci duk wadanda aka bayar da umurnin cafke su.