Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, kan wani bincike da ake yi kan badakalar kudaden da suka kai Naira Biliyan 8,069,176,864.00.
Sirika wanda ake zargin ya bayyana a ofishin Hukumar EFCC na Babban Birnin Tarayya da misalin karfe 1:00 na ranar Talata.
A lokacin da Sirika ya isa ofishin hukumar EFCC, an rahoto cewa, yana fuskantar tambayoyi daga jami’an EFCC game da badakalar bada kwangilar da ya ba wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited, mallakin kaninsa, Abubakar Sirika.