Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti, EFCC ta saki Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris da aka dakatar.
Wata majiya daga danginsa, sun tabbatar wa DAILY NIGERIAN sakin sa, inda suka ce an sako Ahmed ne a daren Laraba.
Jami’an EFCC sun kama Ahmed Idris ne a ranar 16 ga watan Mayu bisa zargin karkatar da kudade Naira biliyan 80.
Kakakin EFCC, yayin da yake tabbatar da kama shi, ya ce ana zargin an karkatar da kudaden ne ta hanyar zuba jari akan gine-gine a Kano da Abuja.
An nada Idris a matsayin Akanta-Janar na Tarayya a ranar 25 ga Yuni, 2015 bayan Jonah Otunla ya bar ofis a ranar 12 ga Yuni, 2015.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp