Mai shari’a Adeyemi Ajayi na babbar kotun birnin tarayya Abuja, ya ci gaba da shari’ar tsohon Akanta Janar na Tarayya (AGF), Ahmed Idris da wasu mutane biyu bisa zargin almundahanar kudi har naira biliyan 109.
An fara shari’ar wadanda ake tuhumar ne bayan kotun ta bayar da belinsu wanda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta amince musu.
Mai shari’a Ajayi a hukuncin da ta yanke, ta bayar da umarnin cewa wadanda ake tuhumar ba za su bar birnin tarayya ba, face da izinin kotun.
Kotun ta yi barazanar soke belin da aka yi wa wadanda ake tuhumar idan suka fita daga hurumin da aka iyakance musu ba tare da izinin kotu ba.
Kotun ta kuma bayyana cewa wadanda ake tuhumar za su sanya hannu kan yarjejeniyar cewa za su bi ka’idojin belin da EFCC ta ba su.
Bugu da kari, Mai shari’a Ajayi ya bayar da umarnin cewa wadanda ake tuhumar su mika fasfo din su na fita zuwa kasashen waje ga hukumar EFCC sannan kuma ba a yarda su sake neman wani sabon fasfo ba, har sai an kammala Shari’a.