Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa tare da wasu shugabanin daga juhohin Arewacin kasar nan Sun kaddamar da wata kungiyar hada Kai da Samar da Zaman lafiya da ci gaban Arewa Mai Suna ( Arewa Cohesion Initiatives For Peace And Development)
Taron Wanda ya gudana a dakin taro na gidan Sardauna dake jihar Kaduna ya samu halarcin malaman addinin musulunci dana kirista da kungiyoyin Matasa da sarakunan Gargajiya da dattawan Arewa daga jihohin 19 na Arewacin kasar nan.
- Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari
- NPA Ta Tarbi Babban Jirgin ‘Ruwa MB Ocean Dragon’ Don Bunkasa Ayyukanta
Da yake kaddamar da kungiyar, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, ya shaida wa taron cewa lokaci yayi da Arewa zata tashi tsaye wajen kawar da rarrabuwar kawuna da kuma sanin makomarta.
“An tsara kungiyar ne domin hada kan Arewa da magance matsalar rashin aikin yi Wanda hakan ya sanya aka tattaro manyan hafsoshin soja da suka yi ritaya, da tsaffin gwamnoni, da masu rike da sarautun gargajiya, da masu fafutukar kare hakkin jama’a, da kungiyoyin matasa, da kwararrun a fannin ci gaban kasa wadanda da yawa daga cikinsu sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da mulki da kuma mayar da muradun Arewa saniyar ware a ‘yan shekarun nan”
“Yankin arewa na iya shawo kan kalubalen da suke fuskanta ta hanyar hadin kai da kuma sabunta kudurin samar da ci gaba,”
Bafarawa ya kuma tabbatar da cewa ba an kafa kungiyar bace a matsayin dandalin siyasa ba, kuma ba ta da shirin rikidewa zuwa jam’iyyar siyasa ba Yana Mai cewa kungiyace ta kawo hadin Kai da ci gaban yankin Arewa.
“Ba mu fito don yakar kowa ba amma don gina tubali da samar da kyakkyawar alaka Wanda kuma Manufarmu ta wuce siyasar bangaranci,” in ji shi.
Bafarawa ya kara da cewa, “Muna son duniya ta ga wani sabon labari da ya kunno kai daga yankinmu, wanda ke ba da kwarin gwiwa da juriya, da sauyi, wanda ke zai nuna cewa Eh, zaman lafiya mai yiwuwa ne da hadin a yankin Arewa”
Tsohon gwamnan ya bayyana mummunan halin da yankin Arewa ke ciki a halin yanzu, inda ya bayyana rashin tsaro da ake fama da shi, da rashin aikin yi ga matasa, da tabarbarewar dabi’u, da kuma talauci Inda yace abin takaici matuka.
Ya ci gaba da cewa kaddamar da kungiyar a daidai wannan lokaci Yana da matukar mahimmanci Domin fuskantar kalubalen da yankin Arewa yake fuskanta.
“kungiyar zata taimaka wajen Samar da Zaman lafiya da daidaito da kuma tattaunawa, hanyoyin da za’a Samar sa ci gaban Arewa ta bangarori daban-daban” in ji Bafarawa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp