Na san da yawa cikin masu bibiyar alamuran dake faruwa a harkokin kasa da kasa, ba su manta da yadda a baya bayan nan kungiyar tarayyar Turai EU, ta fitar da wasu sabbin matakai na kakabawa wasu sassan kasar Sin takunkumi ba.
Wato dai batun nan na yadda a farkon makon nan kungiyar EU ta amince da wasu tanade-tanade na kakabawa wasu sassa 84, da daidaikun mutane na wasu kasashe daban daban takunkumai, bisa zarfin wai suna taimakawa dakarun sojin Rasha da kayayyakin aiki, irin su sassan jirage marasa matuka, da sauran abubuwan harhada naurorin laturoni a rikicinta da Ukraine. Kuma 7 daga cikin wadancan sassa da takunkuman suka shafa sun fito ne daga kasar Sin.
- Sin Da Amurka Za Su Iya Samar Da Alfanu Ga Duniya a Hadin Gwiwarsu
- Da Rancen Naira Tiriliyan 13 Za A Cike Gibin Kasafin Kudin 2025 — Edun
Ba dai wannan ne karon farko da EU ta dauki irin wannan mataki kan wasu sassa ciki har da daidaikun Sinawa ba, kuma a lokuta daban daban, irin wannan mataki kan hada da takunkumin hana tafiye-tafiye, da daskarar da kadarori, da hana damar samar da kudade, matakan da a baya EUn kan ce na shawo kan kalubalen fitar da hajoji ne.
Illar wannan mataki na EU, shi ne tarayyar Turai na aikewa da wani sako mai karfi ga bangaren Sin, cewa kungiyar na zargin Sin da goyon bayan Rasha a rikicinta da Ukraine, duk da sanin cewa wannan zargi ba gaskiya ba ne, kuma mataki ne da ka iya lahanta alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin EU da Sin.
Wani abun lura ma shi ne duk da cewa Amurka ta sha kakkaba wasu takunkumai kan kasar Sin, bisa zarginta da goyon bayan Rasha a rikicinta da Ukraine, takunkuman da kuma suka fi tsauri sama da na EU, ba su sauya matsayar Sin na tsayawa bisa adalci, da kin goyon bayan wani bangare a rikicin bana, don haka ya kamata ita ma EU ta san cewa, Sin ba za ta yi watsi da sahihiyar manufarta ta kin goyon bayan rikici da ingiza sulhu ba. Kuma hakan ba ya nuna cewa Sin za ta yi watsi da gudanar da hada-hadar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da kasar Rasha kamar yadda aka saba tun tuni ba.
A wannan gaba da alkaluma ke nuna yawan takunkuman da EU ta kakkabawa kasar Rasha ma sun kai zagaye na 15, ya dace EU ta lura cewa, ba za a iya warware rikicin Rasha da Ukraine ta hanyar kakkaba takunkumai ba, kuma Amurka ce ke da alhakin ingiza wutar rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Rasha da Ukraine, da ma makamancinsa na Israila da Hamas a Gaza. Don haka, idan har neman wanda za a dorawa alhakin tashe-tashen hankula dake wakana a Turai da Gabas ta tsakiya ake yi, ya wajaba EU ta mayar da hankali ga Amurka, domin jin bahasi, muddin dai ana son tafiya bisa turbar gaskiya da adalci.(Saminu Alhassan)