Dakarun rundunar soji ta ‘Operation Safe Haven (OPSH)’ sun yi gaggawar shiga tsakani a wani lamarin da ake zargi an sanya wa Shanun kiwo na wani Makiyayi guba a filin da suke kiwo a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato, inda aka samu rahoton mutuwar wasu shanu 32.
Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a wani fili da ke kan hanyar Zawura-Jebbu Miango, tsakanin Dutsen Kura da Jebbu Miango, yankin da ke fama da rikicin kabilanci da manoma da makiyaya.
- Tsohon Minista Ya Zargi Isra’ila Da Kasashen Yammacin Turai Da Kitsa Kashe-kashen Rayuka A Nijeriya
- An Kashe Mutane 7 A Yayin Da ‘Yan Ta’adda Suka Ƙaddamar Da Wani Sabon Hari A Adamawa
A cewar majiyar soji, makiyayin da lamarin ya faru da shi, Alhaji Samaila Nuhu, ya kai kara cewa, dabbobin nasa sun fara nuna alamun ban mamaki bayan sun yi kiwo a yankin, lamarin da ya sa yake zargin cewa, da gangan aka sa musu guba.
Dakarun da ke karkashin sashe na 3 na OPSH, da aka tura wurin da lamarin ya faru, biyo bayan kiran gaggawa da aka yi musu, sun tabbatar da cewa, makiyayan sun riga sun yanka shanun da kansu, domin gudun kar a yi asara da yawa. Binciken da aka yi a yankin ya kai ga gano tumatur da ake zargin guba ne da yalon lambu an warwatsa a filin. Kuma babu gidaje a kusa da wurin, wanda hakan ke haifar da zargin cewa, mai yiwuwa wasu da ba a san ko su waye ba ne suka ajiye abun wanda ake kyautata zaton yana dauke da guba.
A martanin da babban jami’in runduna ta 3 kuma kwamandan OPSH, ya jagoranci wata tawaga mai karfi da suka hada da shugaban karamar hukumar Bassa, jami’in ‘yansanda na shiyya, da sauran masu ruwa da tsaki zuwa wurin domin ganewa idanunsu. Ziyarar ta kwantar da yiwuwar tarzoma tare da dakile duk wani harin ramuwar gayya daga al’ummar Fulanin da abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp