A ranar 21 ga watan Disamban shekarar 2022 ne, aka gudanar da taron bunkasa zuba jari na duniya na babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao (GBA) a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.
Bayanai na cewa, an sanya hannu kan ayyuka sama da 800 da suka hada da zuba jari da darajarsu ta kai yuan tiriliyan 2.5 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 358 a wani bikin baje kolin zuba jari a lardin Guangdong, wani abin da ke nuna kwarin gwiwar masu zuba jari na duniya, kan tattalin arzikin kasar Sin, duk da tasirin annobar COVID-19 da duniya ke fuskanta.
Taron na daga cikin manya al’amuran inganta zuba jari da aka gudanar a kasar Sin, tun bayan da kasar ta dage matakan yaki COVID-19 da dama a watan Nuwamba da Disamba, wanda ke kara fatan sake farfado da harkokin zamantakewa da tattalin arziki.
Masana na cewa, duk da tasirin COVID-19 da wasu matsaloli da ake fama da su a duniya, kasar Sin ta ci gaba da janyo ‘yan kasuwa na ketare, saboda babbar kasuwarta da ke ci gaba da bunkasa, da yadda take ci gaba da bude kofa ga kasashen ketare, da managartan tsarin masana’antu.
Alkalumman hukuma sun nuna cewa, jarin kai tsaye da aka zuba a babban yankin kasar Sin, a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2022 da ake amfani da shi, ya kai dalar Amurka biliyan 168.34, wanda ya nuna karuwar kashi 17.4 bisa makamancin lokaci na shekarar 2021. (Ibrahim Yaya)