A yau Alhamis, kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, layin dogo na kasar Sin ya gudanar da balaguron fasinjoji miliyan 23.13 a jiya Laraba, wato ranar farko ta hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na tsawon kwanaki 8.
A cewar kamfanin sufurin jiragen kasan, wannan adadi ya nuna wani sabon tarihi na yawan balaguro da aka samu a rana daya.
Kamfanin sufurin jiragen kasan ya yi kiyasin cewa, za a yi tafiye-tafiye miliyan 19.3 a ranar Alhamis, tare da karin jiragen kasa 1,409 da aka samar. Yayin da bikin tsakiyar kaka ya fado lokaci guda tare da ranar kafuwar PRC a wannan shekarar, ana sa ran hutun da ake yi na kwanaki takwas zai haifar da karuwar bukatun balaguro sakamakon yawan zuwa yawon bude ido da kuma ziyarce-ziyarcen dangi.
A cewar ma’aikatar sufurin kasar, ana sa ran gudanar da balaguro kusan biliyan 2.36 a duk fadin kasar Sin a lokacin hutun, inda aka kiyasta yawan tafiye-tafiyen a kowace rana za su kai miliyan 295, wanda hakan ke nuna karuwar kashi 3.2 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2024. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














