Rahotanni sun bayyana cewa, akalla kimanin mutum takwas (8) ne suka gamu da ajalinsu yayin da karin wasu da dama suka samu raunuka, sakamakon fashewar nakiyar da ake zargin an binne a hanyar Maiduguri zuwa Damboa.
Ana kyautata zaton Boko Haram ne suka dasa bam din a hanyar, wacce ta kutsa zuwa cikin dajin Sambisa, hanyar dai, dama ta lalace sabida karancin zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyar.
- Shugaban Burkina Faso Ya Yi Fatali Da Tayin Saudiyya Na Gina Masallatai 200 A Kasarsa
- Tsohon Kocin Super Eagles, Christian Chukwu, Ya Rasu Yana Da Shekaru 74
Bam din ya fashe ne a lokacin da ayarin motocin matafiya, tare da rakiyar tawagar sojoji ke kan hanyar daga Damboa zuwa Maiduguri, a yau Asabar 13 ga watan Afrilun 2025.
Wasu karin majiyoyi sun nuna cewa, wannan hanyar ta hada Maiduguri da wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar Borno, wacce ta kasance yankin da yan ta’addan Boko Haram ke yawan kai hare-hare tsawon shekaru.
A baya hanyar, ta kasance a rufe amma Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum ya bude ta, domin bai wa jama’a damar ci gaba da zirga-zirga a yankin da suka hada da Damboa, Chibok da sauran kananan hukumomi a kudancin Borno tare da taimakon rakiyar sojoji a matsayin kariya.
An kwashe wadanda suka rasun tare da wadanda suka jikkata, wanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba, zuwa asibiti a Maiduguri domin samun kulawar likitoci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp