Aƙalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata, sakamakon fashewar bam da aka birne a hanyar Maiduguri zuwa Damboa, a Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a yau Asabar, lokacin da ayarin motocin matafiya da ke tare da rakiyar sojoji daga Damboa zuwa Maiduguri suka taka bam da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka dasa shi.
- Newcastle Na Gab Da Samun Gurbi A Gasar Zakarun Turai
- Sin Ta Yi Allah-wadai Da Karin Harajin Amurka Ta Kuma Jaddada Goyon Bayanta Ga Ka’idojin WTOÂ
Wannan hanya na cikin dajin Sambisa ne, kuma an fi samun hare-hare a cikinta saboda kasancewarta hanyar da ta kai zuwa wuraren da ‘yan ta’addan ke fakewa.
Wata majiya ta ce hanyar na haɗe Maiduguri da wasu ƙananan hukumomi kamar Damboa da Chibok da ke kudancin Jihar Borno, yankin da ke fama da hare-haren Boko Haram na tsawon shekaru.
A baya, an rufe hanyar saboda rashin tsaro, amma daga baya Gwamna Babagana Zulum ya buɗe ta domin bai wa jama’a damar yin zirga-zirga, tare da rakiyar sojoji don kare lafiyarsu.
An É—auki waÉ—anda suka mutu da waÉ—anda suka jikkata zuwa asibiti a Maiduguri, inda ake ba su kulawar.
Har yanzu dai ba a tantance yawan waÉ—anda suka jikkata ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp