‘Yan sa-kai biyu sun rasa rayukansu yayin da wani bam da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka dasa a ƙaramar hukumar Gujba ta Jihar Yobe.
Masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Satumba, a kan hanyar Damaturu–Buni Yadi, kusa da ƙauyen Madiya.
- Kasashen Sin Da Afrika Za Su Hada Kai A Bangaren Intanet
- Kotu Ta Dakatar Da PENGASSAN, NNPCL Kan Katse Wa Matatar Ɗangote Ɗanyen Mai Da Iskar Gas
Bam ɗin ya tashi da misalin ƙarfe 2:30 na rana, inda ya kashe mutanen nan take.
An gano waɗanda suka mutu; Kinnafi Modu mai shekara 35 da Mamman Kasaisa mai shekara 27.
Wasu ‘yan sa-kai biyu kuma sun ji munanan raunuka, inda aka garzaya da su Asibitin Gwamnati na Damaturu.
Jami’an ’yansanda da na leƙen asiri sun kai ziyara wajen, sun taimaka wajen kwashe gawarwakin waɗanda suka rasu.
An ƙara tsaurara tsaro a kan hanyar don hana ƙara kai wasu hare-hare.














