Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya bayyana cewa bai taba goyon bayan dokar gyaran haraji dari bisa dari ba, inda ya bai wa jama’a hakuri kan lamarin.
Ya ce: “Abin da na fada shi ne, akwai abubuwa da dama a cikin dokar da za su amfani Arewa da Nijeriya baki daya.
- Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da CBN Daga Sallamar Ma’aikata 1000
- Adadin Zirga Zirga Ta Jiragen Kasa A Sin Ya Haura Biliyan 4 A Watanni 11 Na Farkon Bana
“Mu, ‘yan Majalisar Arewa, ya kamata mu yi amfani da rinjayenmu wajen tabbatar da cewa duk abin da zai amfani yankinmu mun goyi bayansa.
“Idan kuma akwai wani bangare da zai cutar da mu, sai mu gyara ko mu cire shi.”
Wannan bayanin na cikin wata takarda da ya fitar a Kano a ranar Laraba.
Ya kara da cewa: “Ya kamata mu yi amfani da wannan dama wajen bijiro da wasu dokoki da za su amfani Arewa, a kuma tabbatar da cewa an yi wa sauran jihohi adalci.
“Amma wasu na ganin ya kamata a yi watsi da dokar gaba daya.”
Kofa ya jaddada cewa: “A matsayina na wakili, ban taba goyon bayan wata doka da za ta cutar da al’ummata ba, kuma ba zan taba yi ba,” in ji shi.
“Duk wanda ya ji haushin matsayata, ina ba shi hakuri, musamman abokan aikina ‘yan majalisa, Sanatoci, gwamnoni, shugabanni, sarakuna, malamai, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa, ‘yan boko, ‘yan jarida, mata da matasa. Allah Ya kara mana fahimta.”
Ya kuma gode wa jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa shawarwari da goyon baya da yake ba shi, tare da gode wa Alkali Salihu Abubakar daga Jamila Zariya bisa jajircewarsu wajen faɗakarwa.
“Zan ci gaba da kokarin ganin ba a cutar da Arewa ba, kuma an yi wa kowa adalci a Nijeriya,” in ji shi.