Kadan daga cikin bayanan kalubalen da jarumar HALIMA YAKUBU ADAM wacce aka fi sani da LEEMAH BULTUWA ta fuskanta game da harkar fim inda ta bayyana wa masu karatu, Leema Bultuwa daya ce daga cikin jaruman fina-finan Hausa da ke masana’antar Kannywood.
Idan masu karatu na biye da mu za ku ji wasu batutuwan masu yawan gaske wadanda jarumar ta bayyana muku game da rayuwarta da kuma sana’arta ta fim. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki
Sunana Halima Yakubu Adam, wacce aka fi sani da Leemah Bultuwa.
Me ya sa ake kiranki da Leema Bultuwa
Na fito a wani fim ne Shakundun to, sunana Bultuwa a cikinsa da yake fim ne na barkwanci
Masu karatu za su so su ji dan takaitaccen tarihinki
Sunana Halima Yakubu Adam kamar yadda na fada a farko, an haife ni a Dan Agundi, na girma a unguwar Sharada, na yi makatantar Boko da ta Islamiyya duk a garin Kano, na yi karatun addini me zurfi inda na yi saukata ta farko ina shekara13, na yi sauka ta biyu ina shekara 15, na hada hadda ta ina shekara 20, bangaren boko kuma yanzu shekarata biyu da gama FCE Kano.
Ya batun iyali, shin kin taba aure ko tukunna dai?
Na taba aure inada yaro guda daya sunansa Affan shekararsa shida 6.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Labari ne me tsayi, shi fim din burina ne tun ina karama nake san fim sai dai a gida basu amince ba har aka yi min aure, auran ya mutu Allah dai ya yi ina da rabo aka barni, amma fa gaskiya na sha wahala kan su amince a gida, wahala ba fa ‘yar karama ba. Amma yanzu da suka fahinci ita harkar fim yadda ka dauke ta haka za ta tafi da kai, shike nan tunda a duniya duk inda ka samu kanka to, tarbiyyar gidanku ita ce za ta yi aiki.
Lokacin da ki ka fuskanci kalubale daga wajen mahaifanki, shin kin shiga harkar ne kai tsaye ganin hakan ya sa suka hakura ko kuwa bari ki ka yi har sai da suka amince tukunna ki ka shiga?
Sai bayan da suka amince sannan na fara gaskiya, sabida ba hakura nayi da rokonsu ba, cigaba na yi da naci har Allah ya taimake ni aka barni.
Ya Gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Ni gaskiya ban fuskanci matsala ba, saboda Ibrahim Bala yayana ne ya tsaya min a kan komai, dan ina yin rijista washegari aka fara dora mun ‘camera’.
Kina nufin Ibrahim Bala dan’uwanki ne na ji ni, ko ya ki ke nufi?
Yayana ne kuma gata na.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?
Zan yi shekara biyar da fara fim.
Ya farkon farawar ta kasance?
Na fara a sa’a gaskiya Alhamdullahi ina farawa cikin izinin Ubangiji duk wani abu da ake bukata zan yi shi, kuma bana dauka wasa ne ina dauka kawai gaske ne, ban sha wahalar komai ba a wannan bangaren.
Da wane fim ki ka fara?
Wani fim ne sunansa zaman gida a mahaukaciya na fito ‘coronabirus’ suke ce min da ya ke lokacin zaman gida aka yi shi.
Lokacin da ki ka ji cewa za ki fito a mahaukaciya cikin shirin, shin baki ji wani abu ba?
Na ji sosai ma, amma ana yi min kwalliyar mahaukaciyar kawai sai na ji ai kamar mahaukaciyar ce ni.
Fim din ya fita ko kuwa har yanzu ba a saki aikin ba?
Arewa24 sun karba, amma har yanzu basu saka shi ba, sai dai tallansa da aka saki.
Bayan sakin tallan shirin da aka yi kin samu wani kalubale daga wajen mutane musamman wadanda suka sanki, kawaye ko mutanen unguwa ko kuma ‘yan’uwa?
Magana kam an yi ta har nuna ni aka rika yi ana cewa “ji beta, a fim din ma a rasa a me za a saka ta sai a mahaukaciya” an yi surutu sosai, a gida dai dariya aka rinka yi min.
Ko za ki iya tuna nawa ne adadin finafinan da ki ka fito ciki?
Akwai irin su; Mata Dozin, ‘Yar Tsakar Gida, Shakundun , Sirrin Boye, Mayafin Sharri, Acikin Biyu, Gidan Danka, Kantakile, Mekirinki, Matar Megari, Zaman Gida, Ranar Suna, Da dai sauransu na manta gaskiya.
Idan aka ce ki zabi guda wanda ki ka fi so cikin wadannan finafinan da ki ka fito, wanne za ki dauka kuma me ya sa?
Gaskiya duk cikinsu ba wanda bana so, ina sansu sosai kuma ina alfahari da su.
Wane fim ne a ciki ki ka sha wahala wajen daukarsa, kuma wanne ne ya fi saka ki dariya a ya yin daukar shirin?
Shakundun, saboda gaskiya na sha wahala kuma na yi dariya sosai, duk girman nan nawa a cikin fim din shekarata sha uku 13, kuma ni shagwababbiya ce a ciki, babana Musa Mai’Sana’a ne to an shafa min abubuwa a fuskata aka maida ni baka, kuma an cire min hakori na na gaba guda biyu na sha wahala sosai, kuma shi ya sa sunan Bultuwa ya bi ni, saboda ta dalilinsa aka sanni sosai.
A cikin shirin aka cire miki hakoran gaba guda biyu?
Eh! amma fenti aka yi musu, sai suka zama kamar babu
A zahiri ina da shagwaba gaskiya, kiin ga a Mata Dozin ma a shagwababbiya na fito, kawai cewa ake rol din zai yi min kyau, kuma in aka ba ni ina yi yadda suke so, dan yanzu haka abun ya riga ya gama bin jikina gaskiya.
A cikin fim din Mata Dozin wane waje ya fi burge ki?
Dukka komai da na yi yana burge ni, amma da wani waje dana yi wa yaya Ibrahim rashin kunya sun zo zance yadda na yi na ga kokarina, saboda mantawa nayi da waye shi a wajena nayi masa rashin kunya. Sai kuma inda na kawo kwarto gidan mijina to wajan ya daga min hankali har yanzu idan na tuna bana jin dadi, kuka nake yi.
Me ya ke saka ki kuka game da hakan?
Abin da ya sa na ce ina yin kuka a kai shi ne; na kawo kwarto a cikin fim din kuma Yaya Ibrahim ne a ciki sai nake ganin abun kamar da gaske wai na kawo kwarto kuma an kama ni da shi, har yanzu abun yana tayar mun da hankali. Akwai ranar da na je zan shiga gidan sarki kawai wani mutumi ya taso “kun ganta wallahi ita ce tsinanniyar nan da ta kawo kwarto dakin aure, ba su san darajar aure ba” wallahi haka ya taso gabana yana cewa “Ke tsinanniya ce, la’ananniya, kin kawo kwarto dakin mijink𝗶, baku san darajar aure ba, Allah ya tsinewa mata irinku”, na ce masa “Baba fim ne”, ya ci gaba “fim din a fim din amma kin bawa kwarto hijabi da nikab” wallahi yadda ki ka ji haka, haka ya fada mun a cikin mutane zan shiga gidan sarki. To, lokacin da aka yi aikin sai da na kai kusan sati daya ina tunani har rashin lafiya na yi saboda wannan kwarton, saboda na yi kuka sosai har cikin raina na ji abun to, kuma na kara haduwa da wannan mutumin shi ma ya gaya mun wannan maganar to, abun ya tayar mun da hankali ban san ya mutane suka fuskanci al’amarin ba.
Ya batun ci gaba da fitowarki cikin shirin musamman yanzu da ake kokarin fitar da zagaye na biyu, shin za ki ci gaba da fitowa a shirin ko kuwa kin hakura saboda kalubalen da ki ke fuskanta game da shirin?
Ina nan a kan baka na, babu gudu ba ja da baya gaskiya, ko yanzu aka dawo dora wa za mu yi da salo kala-kala yanzu ma aka fara.
Ya ki ke kalon ci gaba da fitowarki cikin irin wannan rol din a sauran finafinai, bakya ganin hakan zai iya janyo miki wani kalubalen da ya fi wannan?
Ko yanzu aikin ya zo yi zan yi sana’a ta ce ai, ba wai gaske ba ne.
Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?
Da yawa gakiya, na samu abubuwa da yawa masoya sun yi min kyauta kala-kala, sannan na samu alfarma da yawa saboda fim.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta cikin masana’antar musamman ga abokan aikinki?
Gaskiya dai babu saboda ni ba mace ce me shiga mutane ba, aiki ne kawai ya ke fitar da ni a gida.
Ya ki ka dauki fim a wajenki?
Na dauki fim sana’a ce me tsafta, kuma in mutun ya rike ta zai cinma dukkan burinsa na rufin asiri.
Ya yanayin mu’amularki da sauran mutanen unguwa kawaye da abokan arziki a yanzu?
Ba ni da kawaye da yawa su uku ne, unguwar mu kuma ni ba fita nake ba kuma bana shiga makota koyaushe ina cikin gida sai in zan fita aiki.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
Duk inda na je an sanni kawai daukaka ce, ita kuma lokaci ce, amma ko yanzu aure ya taso gaskiya yi zan yi.
Ko akwai wanda ya taba cewa yana son ki cikin masana’antar wanda har ta kai da kin fara soyayya da shi?
Gaskiya dai babu ban taba soyayya da dan cikin masana’anta ba.
Misali wani ya ce yana son ki zai aure ki cikin masana’antar, shin za ki amince ki aure shi ko kuwa ba ki da ra’ayin hakan?
Ah, indai da aure ne ai zan iya amincewa, da fahimtar juna tsakaninmu sosai ana aure.
Wane jarumi ko jaruma ke burge ki cikin masana’antar, kuma me ya sa?
Jarumi na Ibrahim Bala, jarumata Aisha Humaira, saboda su din mutanan kirki ne kuma kome zan yi ina dubansu sosai.
Wane irin abinci da abin sha ki ka fi so?
Taliya da Miyar Jajjage da Kifi sai Kunun Aya.
Wane irin kaya ki ke son sakawa?
Ina son saka Atamfa.
Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga fim har ma da wadanda ke ciki?
Shawarata; Indai kin san za ki kare mutuncin kanki to ki shigo, amma indai ba za ki iya kare mutuncinki ba to ina baki shawara ki yi zamanki a gida shi ne gaskiya. Na ciki kuma shawarata gare su su sani ita daukaka lokaci ce kuma nan gaba da aure da haihuwa ko baki kare mutuncnki dan kanki ba to kiyi dan yaran da basu ji ba basu gani ba.
Me za ki ce da masoyanki?
Ina matukar kaunarsu kuma zan ci gaba da nishadantar da su.
Me za ki ce da makaranta shafin Rumbun Nishadi, har ma da ita kanta Jaridar Leadership Hausa?
Masu karanta hirar nan ku sani rayuwa kaddara ce kowa da irin tasa, amma wannan kaddarar tawa ina matukar alfahari da ita. Jaridar Leadership Hausa kuma ina yi muku fatan alkairi kuma nayi farincikin kasancewa tare da ku.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina gaishe da Yayana Ibrahim Bala, ina gaida Anti na Aisha Humaira, ina alfahari da kamfaninmu ALKHAUSAR.
Muna godiya ki huta lafiya
Ni ma na gode sosai