Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya ce, bai saci ko sisi a cikin asusun gwamnatin jihar ba domin sayen gida a daular labarawa kamar yadda wasu takwarorinsa suka yi ba.Â
Ya ce, ya mallaki gida kwaya daya da ke a Unguwan Sarki bayan da ya zama gwamnan jihar kuma gidan ne daya tilo da har yanzu yake cikin shi.
El-rufai ya sanar da hakan ne a wani shirin gidan radiyo na KSMC mallakar gwamnatin jihar, inda kuma ya yi ikirarin tona asirin tsofaffin gwamnonin da suka wawure asusun gwamnatin jihohin da suka shugabanta a baya.
Gwamnan ya yi gargadin cewa, in har suka ci gaba da yin magana, bai da wani zabi da ya wuce na ya sheda wa duniya sunayen tsofaffin gwamnonin da suka wawure asusun gwamnatin jihohin da suka shugaban ta a baya suka kuma yi amfani da kudaden wajen sayen gidaje a daular larabawa da kuma sayen kadarori a kasar Amurka.