Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba ya nadamar cire tallafin man fetur da ya yi tun farkon mulkinsa.
A wata hira ta musamman da ya yi da manema labarai, Tinubu ya ce matakin cire tallafin ya zama dole don hana kasashe maƙwabta cin moriyar albarkatun Nijeriya ba tare da biyan farashi mai tsada ba.
- Yawan Kai-Komon Mutane Tsakanin Lardunan Sin Zai Kai Kimanin Biliyan 64.5 A 2024
- Sin Ta Fitar Da Dokar Mayar Da Martani Da Za Ta Shafi Wasu Kungiyoyi Da Jami’ai Na Kasar Canada
Shugaban ya kuma ce yana ƙin tsarin kayyade farashi, inda ya yi alƙawarin samar da isasshen mai a kasuwa don biyan buƙatun jama’a.
Cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023 ya haifar da hauhawar farashin mai daga Naira 200 zuwa sama da Naira 1,000 a lita, wanda ya janyo matsananciyar tsadar rayuwa ga ‘yan Nijeriya.
Duk da haka, Tinubu ya jaddada cewa sauye-sauyen da ya kawo na nufin ƙarfafa tattalin arziƙi a nan gaba.
A kan batun haraji, shugaban ya ce ba zai janye sabon ƙudirin dokar haraji ba, duk da adawar da ya fuskanta.
Ya bayyana cewa dokar za ta tallafa wa masu rauni kuma za ta haifar da ƙarin kuɗaɗen shiga ga gwamnati.
Game da tsadar rayuwa da kuma hauhawar farashin kayayyaki, Tinubu ya ce Nijeriya tana kan turbar ci gaba, yana mai ikirarin cewa an samu ci gaban tattalin arziki ba tare da dogaro da kuɗaɗen kamfanin NNPCL ba ko lamuni daga babban bankin ƙasa.