Mataimakin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Kashim Shettima ya bayyana cewa bai zabi Bola Ahmad Tinubu ba don ya dauke ni a mataimakinsa a zaben 2023.
Ya ce, Asiwaju Bola Tinubu mutum ne da ke kishin gina Nijeriya, nima hakan zuciyata take, shi yasa na zabe shi.
Kashim Shettima ya sanar da hakan ne a taron gabatar da shi a matsayin mataimakin Tinubu da aka gudanar a Abuja a jiya Laraba, inda ya kara da cewa ba wai ina son in zama mataimaki don na wakilci alummar Musulmai ba, sam ba haka abin yake ba, idan har hakan abin yake, ina ganin Sultan na Sokoto ne ya fi cancanta da hakan.
A cewarsa “ban nemi in zama a dauko ni mataimakin ba don in kare ra’ayoyin Hausawa da Kanuri ba, sam abin ba haka yake ba.”