Bayanai sun fara fita wo fili kan zargin da ake yi na cewa, jam’iyyar APC ta dauko wasu malam addinin Kirista wato Bishop-Bishop, maza da mata don su halarci gabatar da Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Bola Tinubu, bayan da daya daga cikin malaman da aka gayyata, Joseph Odaudu, ya fasa kwai.
A jiya Laraba ne Tinubu ya gabatar da Sanata Kashim a Abuja, inda wani faifan bidiyon da ya yi ya yawo a kafafen sada zumunta, ya nuna malaman sanyen da rigunansu na ibada suna ta tururwa zuwa shiga taron.
- ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Shugaban Jam’iyyar APC A Edo
- Da Dumi-Dumi: Sheikh Abduljabbar Ya Nemi A Sauya Masa Kotu
Har yanzu dai, APC na ci gaba da shan suka daga wasu sassan kasar nan kan zargin dauko hayar malaman, inda suka danganta hakan a matsayin yunkurinta na samun goyon bayan Kiristocin kasar a 2023.
Joseph Odaudu, ya shaida wa kafar yada labarai ta Peoples Gazette cewa, “An dauke mu gaba daya daga inda ake ajiye motoci da ke a bayan filin Eagle Square inda ‘ya’yan jam’iyyar APC suka yi alkawarin za su bai wa kowannenmu N100,000, amma a karshe suka buge da bai wa kowa N40,000, wasu kuma N30,000 aka ba su.
“Sun zo mana da abinci suka kai mu wani waje suka kuma ba mu kayan muka sanya tamkar mu shugabannin addini ne.”
Sai dai, daraktan yada labarai da samar da bayanai, Bayo Onanuga na ofishin yakin neman zaben Tinubu (TCO), ya karyata ikirarin na Bishop din, inda ofishin ya kara da cewa, malaman addinin ba hayar su aka yi ba kuma su malaman addini ne na kwarai.