Tsohon Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya ce bai taɓa tsanar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ba.
Ya bayyana cewa ya yi suka ne kawai saboda gwamnatin Buhari ba ta ɗauki matakin da ya dace kan matsalar tsaro da ke addabar jiharsa a lokacin.
- Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
- PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
Yayin da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, Ortom ya ce dole ya fito ya faɗi gaskiya domin kare rayukan mutanen da yake wakilta.
“Ban tsani Buhari ba, ban tsani gwamnatinsa ba, kuma ban tsani kowane Bafulatani ba,” in ji Ortom.
“A matsayina na gwamna, nauyi ne a kaina na kare lafiyar mutane na da walwalarsu.”
Ya ce ya dinga ƙorafi ne domin gwamnatin Buhari ba ta ɗauki matakin da ya dace ba game da kashe-kashen da ake yi a Benuwe.
“Ba zan iya zama na yi shiru ina ci gaba da binne mutane ba. Dole ne na faɗi gaskiya,” in ji shi.
“Amma ban tsaya a magana kawai ba, gwamnatina ta kawo hanyoyin magance matsalar da muka ga za su taimaka.”
Ortom ya ƙara da cewa da gwamnatin Buhari ta karɓi shawararsa kuma ta yi aiki da ita, da matsalar tsaro a Benuwe ta ƙare.
Ya ce ya sha kokawa a lokacin, kuma shirye-shiryen da gwamnati ta kawo kamar Ruga ba su da amfani.
Ya ce ba wai rikici ne tsakanin makiyaya da manoma kawai ba, wasu daga cikin makiyaya suna kai wa ƙauyuka hari, suna kashe mutane, lalata gonaki, yi wa mata fyaɗe da aikata wasu laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp