Babban Ministan Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewar bai yi nadamar yakar jam’iyyarsa ta PDP a zaben 2023 da ya gudana.
Wike, ya bayyana haka ne cikin shirin siyasa na gidan talabijin a ranar Laraba.
- Dorewar Bunkasuwar Tattalin Arzikin Sin Ta Karawa Duniya Kwarin Gwiwa
- Da Ɗumi-ɗumi: Kamfanin NNPCL Ya Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa Naira 1,030 Kowace Lita A Abuja.
A gefe daya kuma, ya musanta zargin saba wa dokokin jam’iyyar saboda kin taimaka wa dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar.
Ya kare matsayarsa, inda ya ce ya yanke shawarar yin hakan ne saboda tabbatar da gaskiya da adalci.
Wike, ya hada kai da wasu gwamnonin PDP hudu da aka sabawa, da suka hada da Samuel Ortom na jihar Benuwe da Seyi Makinde na jihar Oyo da Okezie Ikpeazu na Abiya da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu domin yakar takarar Atiku.
Gwamnonin biyar sun dage a kan matsayarsu ta sai an sauke Sanata Iyorchia ayu daga kan kujerar shugabancin jam’iyyar PDP, kafin su mara wa Atiku baya a takararsa.
Atiku ya sha kayi a zabaen a hannun shugaba Bola Tinubu, wanda daga bisani shugaban ya nada Wike a matsayin ministan birnin tarayya.
A farkon makon nan a wani taro da shugabannin PDP suka yi an tashi baram-baram, inda aka sami rabuwar kai.
A yayin taron shugabannin na PDP sun nuna wa juna yatsa kan wanda yake da alhakin jefa jami’yyar cikin rikici tsakanin Atiku da Wike.