Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce, biyaya ga doka da oda ne kawai zai sanya ba za su shiga har cikin gidan gwamnatin jihar Bauchi su kwato mulkinsu da ya suka ya bari ba.
Adamu ya ce, tun asali jihar Bauchi da al’umarta masoya jam’iyyar APC ne, don haka ya nuna kwarin guiwarsa na cewa za su yi wa PDP tumbur a zaben 2023 da ke tafe.
- “Ba Zamu Raba Wa Mata Da Matasa Akuyoyi Da Sunan Tallafin Sana’a Ba A Bauchi” —Sadique
- Ina Jin Takaici Da Damuwa Kan Yadda Ake Fita Daga Jam’iyyarmu Ta APC —Abdullahi Adamu
Abdullahi Adamu wanda ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar ranar Alhamis lokacin bikin kaddamar da yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC tare da mika tutar jam’iyyar ga Air Marshal Sadique Baba Abubakar.
An gudanar da taron a filin wasa na jihar Bauchi, taron kuma ya samu halartar dumbin jama’a daga ciki da wajen jihar.
Adamu ya ce, “Da so samu ne ni Abdullahi Adamu da zan ce ku shiga ku kwato gwamnati da karfin tsiya, to amma saboda sanin doka zamu bi doka, zamu bi ka’ida, kuma in Allah ya so ya yarda, gwamnatin nan ta jihar Bauchi zata tabbata a hannun Air Marshal Sadique Baba Abubakar,”
“A jihar Bauchi mun yi barin mulki, mata za su fi mu sanin bari, to mun yi barin mulki. Gwamnatin Bauchi, Gwamnatin APC ce, ko ba haka ba ne? In kuwa haka ne ya aka yi yau Mulki ba ya hannunmu? Ko me ma ya faru, cikin ikon Allah lokacin sake sabon zubi ya yi, za a yi sabon zabe.
“Ranar 25 ga watan Afrilu za a yi zaben shugaban kasa wanda dukkaninmu hankalinmu ya taru mu zabi Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya. In Muna son a yi tafiya mai riba ya kamata idan muna da shugaban kasa dan APC to a samu gwamnan Jiha dan APC.
“Mu yi wa kanmu adalci mu samu dan APC a gidan gwamnati a ofishin gwamnan Jihar Bauchi, wannan bawan Allah kuwa shi ne, Air Marshal Sadique Baba Abubakar.” Cewar Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu.