Kwatankwacin adadin kudin da kasar Sin ta samu daga shige da ficen kayayyaki da hidimomi a shekarar 2023, ya kai kudin Sin yuan triliyan 41.76, adadin da ya karu da kaso 0.2 bisa dari a kan makamancin lokacin a shekarar 2022, lamarin da ya sa kasar Sin ta kasance kasa mafi yawan cinikayyar kayayyaki a fadin duniya a tsawon shekaru bakwai a jere. Haka kuma alkaluman sun nuna cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako a bangaren.
A halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin duniya bai gudana yadda ya kamata ba, harkokin cinikayyar waje na yawancin manyan kasashen da suka ci gaba ta koma baya bisa babban mataki. Amma harkokin cinikayyar waje na kasar Sin sun samu ci gaba fiye da kima, lamarin da zai taimakawa harkokin cinikayya tsakanin kasa da kasa da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya.
- Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Goyi Bayan Kasashen Yammacin Afirka Da Na Sahel
- Sin Ta Zama Kasuwar Sayar Da Kayayyaki Ta Intanet Mafi Girma A Duniya Tsawon Shekaru 11 A Jere
A kwanakin baya bayan nan, asusun ba da lamunin duniya ko IMF a takaice da sauran kungiyoyin kasa da kasa sun daga hasashen da aka yi kan karuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2023, inda aka kimmanta cewa, gudummawar da kasar Sin ta bai wa karuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2023 ta kai kusan kaso 30 bisa dari, wato ta ci gaba da kasancewa babban karfin dake raya tattalin arzikin duniya. Kuma karuwar tattalin arzikin kasar Sin tana kara habaka bukatun shigo da kayayyaki kasar, da ma na fitar da kayayyaki zuwa ketare. (Mai fassara: Jamila)