Alkaluman masana’antu sun nuna cewa, a cikin watan Maris, ayyukan hada-hadar sayayya ta yanar gizo na kasar Sin, sun ci gaba da samun sakamako mai kyau, inda aka samu daidaito a fannonin bukatu da samar da kayayyaki.
Wani binciken hadin gwiwa da kungiyar hada-hada da sayayyan kayayyaki ta kasar Sin da babban kamfanin cinikayayya ta yanar gizo na JD.com suka gudanar, ya nuna cewa, ayyukan bibiyar harkokin kasuwancin zamani sun karu da maki 1.1 daga watan Fabrairu zuwa maki 108.3 a watan Maris, kusa da mafi girman matsayi a shekarar 2022..
Takwas daga cikin manyan alkaluma 9 da ke auna ayyukan hidimar kasuwancin yanar gizo a fannoni daban-daban, ya nuna ci gaban da aka samu a watan da ya gabata, inda masu manyan kasuwanci da ma kasuwancin yankunan karkara suka karu da maki 1.7 da maki 4.4, bi da bi, daga watan na Fabrairu.
Binciken ya kuma yi hasashen cewa, alkaluman za su ci gaba da karuwa a cikin watan Afrilu, bisa la’akari da cewa, ana sa ran samun karuwar bukatu, kuma akwai gagarumin tasiri a bangaren samar da kayayyaki, yayin da kasar ke kara inganta matakan farfado da tattalin arzikinta. (Ibrahim)