Harkokin jigilar kayayyaki a bangaren cinikayya ta intanet a kasar Sin, sun samu tagomashi a watan Fabreru, yayin da harkokin kasuwanci ke kara farfadowa cikin sauri.
Wani nazari da hadaddiyar kungiyar masu jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin da katafaren kamfanin J.D (Jin Dong) mai sayar da kayayyaki ta intanet suka gudanar, ya nuna cewa, alkaluman tantance yanayin jigilar kayayyaki a bangaren cinikayya ta intanet, sun kai maki 107.2, karuwar maki 2.6 kan na watan Janairu da aka samu karuwar maki 1.8.
Dukkan ma’aunai 9 na harkokin jigila a bangaren cinikayya ta intanet a bangarori daban-daban, sun samu karuwa a watan da ya gabata, inda yawan harkokin kasuwanci ya kai maki 2.6 yayin da na harkokin kasuwanci a yankunan karkara ya kai maki 1.8.
Wannan rahoto manuniya ce cewa, alkaluman za su ci gaba da karuwa a watan Maris, wanda kuma ke jaddada karuwar bukatar kayayyaki a nan gaba. (Fa’iza)