Alkaluma daga kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin sun nuna cewa, masana’antun kera motoci na kasar sun samu bunkasuwa mai karfi a shekarar 2023.
A cewar kungiyar, a bara darajar masana’antun ta karu da kashi 13 bisa 100 kan na shekarar 2022, adadin da ya zarta kashi 8 bisa 100 kan na masana’antun kera kayayyakin kasar baki daya.
- Sin Ta Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Gaggauta Dakatar Da Ayyukan Soji
- Sin Tana Bunkasa Aikin Gona Tare Da Kyautata Muhallin Halittu
Adadin kudaden shigar bangaren, ya kai kudin Sin RMB yuan tiriliyan 10.1, kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.42 a shekarar 2023, wanda ya haura kashi 11.9 bisa 100, idan aka kwatanta da na shekarar 2022.
Bayanai na nuna cewa, jimillar ribar da kamfanonin dake fannin suka samu, ya karu da kashi 5.9 bisa 100 kan na shekarar 2022, zuwa yuan biliyan 508.63. (Ibrahim)