Rahotanni daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta kasar Sin na cewa, sashen ya yi jigilar fasinjoji biliyan 3.68 a shekarar 2023.
A cewar hukumar, adadin tafiye-tafiyen da aka gudanar a rana mafi yawan zirga-zirgar jama’a a wannan shekara, ya zarce miliyan 20, wanda ba a taba yin irinsa ba, kuma matsakaicin yawan tafiye-tafiyen fasinja a kowace rana, ya zarce miliyan 10.
Haka kuma, bangaren ya yi jigilar tan biliyan 3.91 na kaya a bara, wanda ya kasance mafi yawa a shekarar. (Mai fassara: Ibrahim)