Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayyana cewa, dajarar bangaren aikin noma da masana’antu masu alaka na kasar Sin, ta kai kudin kasar Yuan triliyan 18.44, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.65 a shekarar 2021, wanda ya karu da kashi 10.5 kan na shekarar da ta gabata.
A cewar hukumar, dajarar ta kai kashi 16.05 na GDPn kasar. A ciki darajar bangaren aikin noma, da gandun daji, da kiwo, da kamun kifi ya kai kashi 47.2 na jimillar.
Haka kuma darajar a bangaren sarrafawa da yadda ake samar da amfanin gona da ake ci, da gandun daji, da kiwo, da kayyakin da suka shafi kifi, ya kai kashi 20.9 na jimillar. Yayin da darajar jimillar a bangaren noma, da gandun daji, da kiwo da ayyukan rarraba kayayyaki masu nasaba, ta kai kashi 14 cikin 100 na jimillar.(Ibrahim)