Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ce bangaren sarrafa kayayyaki a kasar Sin ya farfado, inda ya fadada a watan Junairu, bayan koma bayan da ya fuskanta cikin watanni 3 a jere.
Hukumar ta ce alkaluman hada-hada a bangaren sarrafa kayayyaki (PMI), sun nuna cewa, hada-hada a bangaren a kasar Sin ya kai maki 50.1 a watan Junairu, daga maki 47 da ya kasance a watan Disamban bara.
Makin da ya dara 50, na nufin samun tagomashi, yayin da kasa da hakan ke alamta koma baya.
Daga cikin masana’antu 21 da aka nazarta, 18 sun bayyana samun karuwar alkaluman PMI a kowanne wata, yayin da aka kyautata matakan yaki da cutar COVID-19, kana ayyukan samar da kayayyaki ke farfadowa. (Fa’iza Mustapha)