Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Dai Bing ya yi jawabi a gun taron da kwamitin sulhu ya shirya bisa salon Aria, kuma bisa jigon “ajandar matasa da zaman lafiya da tsaro na Afirka” a jiya Litinin inda ya bayyana cewa, Sin ta himmatu wajen kiyaye zaman lafiya da ci gaban nahiyar Afirka, da kara nuna goyon baya ga ci gaban matasan Afirka bisa ayyuka na zahiri, kuma tana fatan kara karfinta na goyon baya ga matasan Afirka a wasu fannoni.
Da farko shi ne matasa za su iya ba da cikakkiyar gundummawarsu, da ingiza a hanzarta warware matsalolin dake jan hankulan duniya sosai ta hanyar siyasa.
Na biyu shi ne dakile rikicin karfin tuwo, ta yadda za a iya rage kawo illa ga matasa. Na karshe dai shi ne kokarin samun ci gaba da zaman lafiya, tare da kara taimakawa matasa. (Safiyah Ma)