Mataimakin wakilin Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga kasashe masu sukuni, da su cika alkawarin samar da kudaden aiwatar da manufofin takaita tasirin sauyin yanayi da suka yi wa kasashen Afirka.
Dai Bing ya yi jan hankalin ne cikin jawabinsa a yayin bude muhawara mai taken “Yanayi da tsaron Afirka na kwamitin tsaron MDD”, inda ya ce ya kamata a taimakawa nahiyar Afirka, wajen magance sauyin yanayi bisa alkawuran da aka dauka bisa bukatun nahiyar.
Jami’in ya ce bai dace kasashe masu sukuni su karya alkawuran da suka yi wa kasashe masu tasowa ba, musamman kasashe matalauta na Afirka, ya zama dole su cika alkawuransu, kuma su tsara sabon makasudin tattara kudade na gamayya, ta yadda kasashen Afirka za su samu kudi isasshe da sakamako na gaske.
Dai ya ce hukumomin hada-hadar kudi na duniya, da asusun kudi na sauyin yanayi, ya kamata su daidaita matakin samar da kudade, su kuma tabbatar da samun daidaiton damar samun kudin sauyin yanayi a Afirka.
Dai Bing ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya su kara taimakawa Afirka a fannonin zuba jari, da fasahohin zamani da basira, su kuma kara karfinsu wajen magance matsalolin da su kan faru a Afirka, da taimakawa nahiyar samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. (Safiyah Ma)