Zaunannen wakilin Sin a Majalisar Dinkin Duniya, Fu Cong, ya bayyana a jiya Litinin cewa, bangaren Sin na goyon bayan gaggauta tsagaita bude wuta a rikicin kasar Sudan don kiyaye fararen hular kasar.
Fu Cong ya ce, bangaren Sin ya yi kira ga dukkan bangarorin da rikicin Sudan ya shafa da su sanya moriyar kasar da ta al’ummar kasar a gaba, su daina yin kiyayya da juna, kuma su cika alkawuransu na kare fararen hula bisa yarjejeniyar da aka cimma a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Kasar Sin tana goyon bayan Ramtane Lamamra, manzon musamman na babban sakataren MDD kan batun Sudan, wajen karfafa hadin gwiwa da kungiyar tarayyar Afrika wato AU da sauran kungiyoyin shiyya-shiyya, don su ci gaba da sassantawa. (Safiyah Ma)