• English
  • Business News
Wednesday, July 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bankin Duniya Da IMF Sun Buƙaci CBN Ya Daƙile Hauhawar Farashi A Nijeriya 

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
in Manyan Labarai
0
Bankin Duniya Da IMF Sun Buƙaci CBN Ya Daƙile Hauhawar Farashi A Nijeriya 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Babban Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) sun yi kira ga Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dage wajen shawo kan hauhawar farashi, wanda ya ƙaru daga kashi 33.6% a watan Nuwamba zuwa 34.8% a watan Disamba.

A yayin wani taron tattaunawa, babban manazarci a Bankin Duniya, Sameer Matta, ya ce wajibi ne CBN ta ci gaba da mai da hankali wajen daƙile wannan matsala. Ya kuma jaddada buƙatar inganta samar da kayayyaki, musamman a ɓangaren noma, da bunƙasa haɗin kai tsakanin karkara da birane, tare da sake duba manufofin haraji a wasu ɓangarori.

  • CBN Ya Ce Bai Tilasta Wa Ma’aikata 1,000 Yin Ritaya Ba
  • An Samu Haɓakar Tattalin Arziƙin Nijeriya A Rubu’i Na Ukun 2024 – CBN

A nasa bangaren, jakadan IMF a Nijeriya, Christian Ebeke, ya yi kira da a samu haɗin kai mai ƙarfi tsakanin manufofin tattalin arziƙi da na kuɗi don tabbatar da nasarar rage hauhawar farashi. Ya yaba wa ƙoƙarin CBN da hukumomin kuɗi na gwamnati wajen daƙile matsalar lamunin kasafin kuɗi da kuma inganta yanayin tattalin arziki.

Ebeke ya jaddada cewa matakan da aka ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma gyare-gyaren darajar Naira suna da mahimmanci, amma dole ne a kare marasa galihu daga illolin da matakan ka iya haifarwa.

Haka zalika, Matta ya ja hankalin gwamnati kan mahimmancin ci gaba da aiwatar da shirin kariyar halin da mutane suke ciki da hanzarta bayar da tallafi ga talakawa.

Labarai Masu Nasaba

Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang

David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC

Ya kuma yi gargadi cewa rashin ɗaukar matakai na gyara tattalin arziƙi zai ci gaba da haifar da asara mai yawa, inda tallafin man fetur da na musayar kuɗaɗe ke laƙume kashi biyar cikin ɗari na GDP na ƙasar. Wannan, in ji shi, babban ƙalubale ne ga cigaban tattalin arziƙin Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: CBNNijeriya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Hisbah Ta Ceto Ƴanmata 16 Daga Hannun Masu Safarar Mutane A Kano

Next Post

Shugaba Xi Ya Yaba Da Ci Gaban Kasar Sin Duk Da Kalubalen Da Aka Fuskanta A Shekarar Dragon

Related

Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang
Manyan Labarai

Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang

2 hours ago
David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC
Manyan Labarai

David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC

4 hours ago
Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano
Manyan Labarai

Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano

17 hours ago
Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara

22 hours ago
Barau, Ganduje Da Wasu Sun Isa Madina Don Halartar Jana’izar Aminu Dantata
Manyan Labarai

Barau, Ganduje Da Wasu Sun Isa Madina Don Halartar Jana’izar Aminu Dantata

1 day ago
Duk Da Farfadowar Darajar Naira, Tsadar Kaya Na Ci Gaba Da Lulawa Sama
Manyan Labarai

Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149

1 day ago
Next Post
Shugaba Xi Ya Yaba Da Ci Gaban Kasar Sin Duk Da Kalubalen Da Aka Fuskanta A Shekarar Dragon

Shugaba Xi Ya Yaba Da Ci Gaban Kasar Sin Duk Da Kalubalen Da Aka Fuskanta A Shekarar Dragon

LABARAI MASU NASABA

Arsenal Ta Sayi Kepa Daga Chelsea

Arsenal Ta Sayi Kepa Daga Chelsea

July 2, 2025
Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang

Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang

July 2, 2025
David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC

David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC

July 2, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu

Rikicin Gonar Gado Ya Yi Ajalin Mutum Ɗaya, An Ƙone Gidaje A Filato

July 2, 2025
An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa

An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya

Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya

July 1, 2025
An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin

An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin

July 1, 2025
Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

July 1, 2025
Kayan Aro Baya Rufe Katara

Kayan Aro Baya Rufe Katara

July 1, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100

Askarawan Zamfara Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Bindiga, Kacalla Ɗanbokolo Ubangidan Turji

July 1, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.