Tun lokacin da aka kafa shi, Bankin Proɓidus ya ci gaba da jajircewa wajen sake fasalin banki ta hanyar ƙirkire-ƙirkire, haɗin gwiwa da kuma hidimtawa abokan ciniki. A cikin ƙasa da shekaru goma, bankin ya rikiɗe zuwa ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin hada-hadar kuɗi a Nijeriya, wanda ke ba da mafita da hanyar ga manya da ƙananan masana’antu.
Bankin Providus ya ci gaba da zurfafa tasirinsa a kan tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar saka jari mai mahimmanci a fannin kasuwanci, abubuwan more rayuwa da sabbin hanyoyin biyan kuɗi. Shirinsa ga ƙanana da matsakaitan masana’antu wanda ke gudana tare da haɗin gwiwar Cibiyar Ci Gaban Kasuwanci (EDC), ya horar da ɗaruruwan ‘yan kasuwa, yana taimakawa wajen gina ƙananan kasuwancin da ke haifar da ayyukan yi da samar da ci gaba. Ta hanyar wannan shiri, bankin ya ba da gudummawa sosai ga burin Nijeriya na ƙarfafa yawan matasanta da kuma ƙarfafa ɓangaren tattalin arziƙin da ba na mai ba.
- Bayan Taron UNGA 80, Shettima Ya Nufi Jamus Don Tattaunawa Da Bankin Deutsche
- Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus
A wani yunƙuri da ke tabbatar da darajar Naira da kuma nuna cewa an samu kwanciyar hankali a kasuwar canji, Bankin Providus ya zama cibiyar hada-hadar kuɗi ta Nijeriya ta farko da ta sake dawo da takardar Naira don yin mu’amalar kasuwanci tsakani ita da ƙasashen duniya. Bankin Providus kuma yana kan gaba wajen tallafa wa tsarin fintech na Nijeriya mai saurin bunƙasa, yana samar da hanyoyin nafi sauƙi na biyan kuɗi a zamanance. Ta hanyar tsarin banki na dijital da tsarin haɗin gwiwar fintech, bankin yana aiki a matsayin wata gada tsakanin bankin gargajiya da hanyoyin fasahar hada-hadar kuɗi na dogon zango, daidai da manufofin Babban Bankin Nijeriya.
A cikin hada-hadar harkokin banki a a wannan zamanin, Bankin Providus yana ci gaba da samar da ingantattun hanyoyin saka hannun jari ga kasuwancin da ke aiki a sassan da ke da muhimmanci ga farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya. Mahimmancinsa a kan inganci ta hanyar nuna gaskiya, da samar da ƙwarewar da ya kamata ga abokan ciniki masu zuba jari na gida da na waje. Bankin Proɓidus yana haɓaka tasirinsa fiye da kuɗi ta hanyar shirye-shiryen da aka mayar da hankali kan al’umma da nufin ƙarfafa matasa, ilimin dijital, da tallafin kasuwanci. Bankin ya ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke gina rayuwa mai ɗorewa tare da haɓaka ci gaba a cikin birane da yankunan karkara na Nijeriya.
Manufar Bankin Providus na bai wa ‘yan kasuwa da ɗaiɗaikun jama’a damar samun ci gaba ta hanyar samar da hanyoyin samar da kuɗi na ci gaba da jan hankali a duk faɗin Nijeriya kuma ta haka ne ya samu karramawar Gwarzon Banki na LEADERSHIP na shekarar 2025.












