A halin yanzu an sanar da cewa, Bankin TAJBank Limited, ya sake samun nasarar lashe kambun gwarzon bankin Musulunci a Nijeriya, bankin ya samu nasarar ne a kan wasu bankuna da dama da suka shiga gasar.
Cibiyar da ta shirya gasar ta bayyana cewa, an ba TAJBank lambar yabon ne sakamakon yadda yake gudanar da aikinsa na bayar da bashi ba tare da ruwa ba da kuma yadda ya kirkiro da tsare-tsaren gamsar da abokan huldarsa a harkokin banki.
A jawabinsa na karbar lamban yabon, shugaban bankin, Hamid Joda, ya yaba wa kwamitin bayar da kyautar a kan karrama su da ta yi , “Hukumar gudanarwa TAJBank na mika godiya gare ku a bisa wannan karramawar a matsayinmu na bankin musulunci mai tasowa a fadin duniya, mun kuma karbi wannan lambar ne sau uku a jere , wannan yana kara karfarfa mana na mu ci gaba da ayyukanmu ba tare da saurarawa ba”, in ji shi.
- Attajiri Abdul Samad Rabiu Zai Karbi Ribar Dala Miliyan 79.4 Daga Kamfaninsa Na Abinci
- Mi’ara Koma Baya: CBN Ya Janye Dokar Cazar Kaso 0.05 A Banki
A nasa jawabin, daya daga cikin wadanda suka kirkiro da bankin, Sherif Idi, ya yaba wa cibiyar tare da abokan huldarsu a bisa karramawar, ya ce za su ci gaba da bullo da sabbin matakai na bunkasa jarin masu hulda da su tare da rike dukiyar abokan hulda cikin amana.”
Kwamitin shirya karramawar ta yaba wa TAJBank an kan aiki tukuru da jajircewa, abin da ya sa ta lashe wannan kambu har sau uku a jere, “Wannan kokari na ku ya taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin Nijeriya ya kuma bayar da gudummawa ga samar da aikin yi ga matasanmu.
Idan za a iya tunawa, TAJBank ce ta lashe gasar gwarzon Bankin musulunci da jaridar BusinessDay ke shiryawa karo na uku a jere, 2021 da 2022 da kuma shekarar 2023 haka kuma bankin ya lashe kyautar gwarzon bankin musulunci na jaridar Leadership na shekarar 2020 da sauran karramawa da dama duk a cikin shekara uku.