A ranar 20 ga watan Nuwamba na shekarar 2023 ne mutuwar mai bayar da umarni a masana’antar Kannywood Aminu S Bono ta girgiza masana’antar baki daya.
Aminu S Bono kamar yadda rahotanni suka tabbatar ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya a wannan yinin bayan ya dawo gida daga wajen aikinsa.
Masana’antar ta Kannywood ta kadu matuka da rasuwar wannan bawan Allah wanda jama’a da dama suka yi wa shaidar zamansa mutumin kirki.
An shaidi Bono da kyautata mu’amala a tsakaninsa da abokan aikinsa,makwabta da sauran al’umma wadanda wani abu na yau da kullum ya hadd su.
Aminu S Bono ya rasu yabar matarsa da ‘ya’ya wadanda daga baya mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya dauki nauyin karatunsu tun daga matakin Firamare har zuwa babbar makaranta da gaba da Sakandire.
Wannan yana daga cikin abubuwan da suka faru a masana’antar ta Kannywood a wannan shekara ta 2023 dake bankwana.