Dan takarar kujerar Shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a zaben da ya gabata, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana jin dadin sa da jajircewa da aka yi wajen kafa matatar Dangote.
Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci matatar man, inda yace “Na yi farin ciki da ziyartar matatar mai ta Dangote, kuma na yi mamakin irin jajircewar da aka yi wajen ganin an kafa ta.”
- An Dakatar Da Jami’in Hukumar NIS Saboda Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi
- Sojoji Sun Sake Ceto Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok
Matatar, mai tace ganga 650,000 a kowace rana (bpd), ginshiki ce da abun alfahari a Nijeriya, Kwankwaso ya yaba da cewa, Matatar wata muhimmiyar kadara ce ta ƙasa wacce dole ne a kiyaye ta daga duk wata barazana.
Ya jaddada mahimmancin matatar, da cewa, “Wannan matatar mai karfin ta ce ganga 650,000 duk rana, tana da mahimmanci ga bukatun makamashi da kwanciyar hankali na tattalin arziki, kuma dole ne a kiyaye ta daga duk wata barazana.”
Kwankwaso ya soki kalaman da shugaban hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa ya yi na barazana ga ingancin matatar, inda ya alakanta ta da kalamai masu kawo cikas ga ci gaban kasa.