Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau cewa barazanar da Amurka ta yi ta kara haraji saboda matakan kasar Sin na takaita fitar da ma’adanan farin karfe na rare earth da kayayyakinsa, ba hanya ce da ta dace ba, tana mai bukatar Amurka ta gyara kuskurenta.
Kakakin ma’aikatar Lin Jian ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na yau, inda ya ce a baya bayan nan, Amurka ta yi ta kaddamar da jerin matakan takaita fitar da kayayyaki da takunkumai kan kasar Sin, lamarin dake illa ga muradun kasar.
Lin Jian ya kuma yi kira ga Amurka ta magance damuwar bangarorin biyu ta hanyar tattaunawa bisa daidaito da girmamawa da moriyar juna, ta kuma tafiyar da bambance-bambancen dake tsakaninsu ta hanyar da ta dace da kare dangantakar kasashen biyu bisa aminci don ganin dorewarta.
Ya kuma ce matakan takaita fitar da ma’adanan farin karfe da Sin ta dauka a baya bayan nan, ba su da alaka da kasar Pakistan. Yana cewa matakai ne da gwamnatin Sin ta dauka bisa doka da oda da nufin inganta tsarinta na fitar da kayayyaki. (Fa’iza Mustapha)