Nahiyar Afirka na fuskantar barazanar samun karancin abinci musamman ta bangaren masara da wake, matukar gwamnatocin nahiyar ba su dauki matakan da suka dace ba.
Wannan bayani na kunshe a cikin rahoton da cibiyar kimiyyar yanayi (CSE) da ke Kasar Indiya ta fitar a makon da ya gabata, a Birnin Nairobi da ke a Kasar Kenya.
- Sharhi: Lokaci Ya Yi Da Tinubu Zai Fuskanci Matsalolin Nijeriya
- Mi’ara Koma Baya-Taylor Ya Koma Alkalancin Gasar ‘Yan Dagaji Ta Kasar Ingila
Rahoton ya kiyasta cewa, kashi 65 cikin dari na kasar noma da ake da ita a wannan nahiyar ta lalace, wanda hakan ya sa manoma ke yin asarar kimanin dala miliyan 68 a duk shekara.
Sama da karni uku, nahiyar ta kasance a kan gaba wajen fitar da amfanin gona, sai dai samun sauyin yanayi ya jawo illa wajen fitar da amfanin gonar.
Nan da 2080, yankunan da ake yin wannan noma wadanda suka bushe da kuma wadanda ba su bushe sosai ba, za su iya fadada daga kadaka miliyan 60 zuwa miliyan 80.
Haka zalika, rahoton ya bayyana cewa, kasar noma mai kyau wadda ake noma masara da wake da ke nahiyar, za ta ragu daga kashi 9 zuwa kashi 20 cikin dari.
A cewar rahoton kalubalen sauyin yanayi zai iya kawo tabarbarewar samun karancin abinci a nahiyar.
Ko shakka babu, wannan zai iya haifar da samun mummunar yunwu, wadda za ta karu da kashi 123 a cikin dari daga 2017 zuwa 2021 a tsakanin kasashe 10 da ke fuskantar kalubalen sauyin yanayi a Nahiyar Afirka.
Bayani a kan irin yanayin muhalin na nahiyar (SOE), ya yi nuni da cewa, kasashen Rasha da Ukraine da suka a kan gaba wajen samar da abinci a kasashen da suka kai kimanin kashi 50 a cikin dari, musamman alkama da masara da sauransu, yakin da kasashen biyu ke ci gaba da yi zai iya shafar samar da abinci a Nahiyar Afirka.