Kokarin samar da wadatacciyar Shinkafar da ake nomawa a Nijeriya na ci gaba da fuskanatar barazana, sakamakon shigo da ita da ake yi daga kasashen ketare.
Har ila yau, tsadar kayan noman Shinkafar da rashin samun cikakken goyon bayan hukumomi da manoman ke fusktanta, na kara zama barazana a wannan fanni.
Wani bincike da Jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna irin jajircewa da kuma kokarin da Manoman Shinkafa ke ci gaba da yi domin ganin ta wadata a fadin wannan kasa baki-daya.
Hakazalika, a bangaren Masana’atun da ake sarrafa Shinkafar da ake nomawa a yankunan Arewa, su ma na ci gaba da kai gauro da mari wajen sarrafa ta da kuma tsaftace ta kamar wadda ake kawowa daga waje.
Wasu daga cikin Masana’antun da ke sarrafa Shinkafar a yankunan sun durkushe, sakamakon karancin samun samfarerar da suke sarrafa, wanda hakan ya jawo rashin ayyukan yi ga masu yin aikin Masana’antun.
Misali, akwai Masana’antar da ake sarrafa Shinkafa ta Jihar Kwara, wadda a halin yanzu ayyukanta ba sa tafiya kamar yadda ya kamata, hakan ya kuma yi sanadiyyar rasa ayyukan da dama na ma’aikatan wannan Masana’anta.
Kazalika, yawan Shinkafar ta gida da ake nomawa a Jihar ta Kwara, ya ragu da kaso mai yawa sakamakon kalubale da suke fuskanta da dama.
Wakazalika, Jaridar ta LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Masana’antar da ake sarrafa Shinkafa a garin Ilori a Jihar Kwara da wadda take a garin Offa na Kudancin Jihar, ba su iya samar da yawan Shinkafar da ake bukata ba, sakamakon rashin noma ta da ba a yi ba da dama a jihar.
Mukaddashin Shugaban riko na Kungiyar Manoman Shinkafa na kasa reshen Jihar Kwara (RIFAN), Mal. Muhammed Salihu, ya tabbatar da koma bayan da ake samu na noman Shinkafa a fadin jihar.
Malam Muhammed, ya dora alhakin samun raguwar noman ne kan yadda Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin aikin noma na (Anchor-Borrowers) da kuma rashin kayan aiki na zamani da ya hada da kamar motar taraktar noma, takin zamani da kuma afkuwar iftila’in ambailyar ruwan sama da aka samu.
Haka zalika, ya sake bayar da misali da alkaluma na tan din Shinkafar da aka noma a jihar, inda ya bayyana cewa, a shekarar 2020 an noma tan 60,000, a shekarar 2021 an noma tan 59,000, inda kuma a shekarar 2022 aka noma tan 25,000.
“A ka’ida kamata ya yi a cikin shekara guda su noma Shinkafa a jihar tasu sau uku, amma sai ga shi sun buge da nomawa sau daya a shekara”, in ji shi.
Har wa yau Mukaddashin Shugaban ya kara da cewa, “Muna fuskantar matsalar ambaliyar ruwa, wanda ke lalata Shinkafar da muka shuka da damuna, akwai kuma matsalar rashin kayan aiki da takin zamani da kuma taraktar yin noma.”
Sannan a cewar tasa, an dakatar da shirin aikin noma na (Anchor-borrowers) tun a shekarar 2021, inda daukacin wadannan matsaloli suka taka rawa wajen koma bayan noman wannan Shinkafa a Jihar ta Kwara.
Shugaban ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar, ta samar wa da Manoman Shinkafar wadataccen takin zamani da sauran kayan aiki, domin ci gaba da samar da wadatar Shinkafar a jihar.
Bugu da kari a wani rahoto da Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito, farashin Buhun Shinkafar Gida a garin Ilorin, ya kai Naira 41,000 sabanin yadda ake sayarwa a baya kan Naira 27,000.