Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu cikin gaggawa a jihar.
Ya kuma bayyana cewa, wannan umarnin na daga cikin kokarin da Gwamnatin ke yi wajen kare rayukan dalibai da ma jama’a a fadin jihar.
Umurnin gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar barazanar tsaro a fadin kasar nan, musamman babban birnin tarayya Abuja, wanda ya tilastawa hukumar kula da babban birnin (FCTA) rufe duk makarantu a babban birnin.
A baya dai Gwamna Sule ya fadada Majalisar tsaro a jihar, bayan tattauna batun kalubalen tsaro da Majalisar ta gudanar a garin Lafiya, ta yanke umarnin rufe duk makarantu a fadin jihar.
An tattaro cewa gwamnan ya shaidawa taron majalisar tsaron cewa gwamnati na da sahihan bayanan sirri da ke nuni da cewa ana iya fuskantar barazanar tsaro a cikin al’ummomin jihar da ke kan iyaka da babban birnin tarayya Abuja kamar Gitata da Umaisha a kananan hukumomin Keffi da Toto.
Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar, Hajiya Fatu Jimaita Sabo, yayin zantawarta da manema labarai, ta bayyana cewa, wannan matakin na daya daga cikin matakan da aka dauka domin tabbatar da cewa gwamnati ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a jihar.