Kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona ta doke abokiyar karawarta Sevilla a filin wasa na Ramon Sanchez Pizjuan dake birnin Seville da ci 4-1 a ranar Lahadi,wasan shi ne wasan mako na 23 a gasar Laliga ta kasae Sifaniya.
Barcelona na kokarin ganin ta rage yawan makin da ke tsakaninsu da Real Madrid wadda ke matsayi na daya akan teburin gasar.
- Ko Barcelona Za Ta Iya Sake Zazzagawa Valencia Ƙwallaye 7 Yau?
- Mbappe Da Bellingham Ba Za Su Buga Wasan Da Real Madrid Za Ta Kara Da Leganes Ba
Lewondowski, Fermin, Raphinha da Eric Garcia ne suka jefa kwallayen da suka samar wa Barcelona duka maki ukun da ake bukata,amma kuma Fermin Lopez ya samu jan kati a wasan bayan yayi keta da gangan.
Barcelona zata karbi bakuncin Rayo Vallecano a wasan mako na 24 a filin wasa na Olympico Luis Companys dake birnin Barcelona, ita kuma Sevilla zata ziyarci Real Valladolid a wasanta na gaba a Laliga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp