Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce Kylian Mbappe da Jude Bellingham ba za su buga wasan daf da na kusa da na karshe da kungiyar za ta buga da Leganes a ranar Laraba na gasar Copa Del Rey ba.
‘Yan wasan biyu, sun kara yawan adadin yan wasan Real Madrid da ke zaman jinya, inda dan wasan tsakiya Eduardo Camavinga, masu tsaron baya David Alaba, Antonio Rudiger, da Eder Militao da Dani Carvajal dukkansu suke zaman jinya sakamakon mabanbantan raunukan da suka samu.
- Daminar Bana: NiMet Ta Yi Hasashen Jinkirin Saukar Ruwan Sama A Jihohin Arewa
- Sin Ta Sanar Da Daukar Matakan Mayar Da Martani A Kan Karin Harajin Amurka
Kyaftin din na kasar Faransa, Mbappe ya ci kwallaye 21 a wasanni 33 da ya buga wa Madrid a dukkanin gasa tun bayan da ya koma Santiago Bernabeu daga Paris St Germain a watan Yuni, yayin da Bellingham mai shekara 21 ya jefa kwallaye har 10 a wasanni 30.
Ancelotti ya shaidawa manema labarai ranar Talata cewa “Bellingham ya samu rauni yayin atisaye amma kuma Vinicius Jr zai buga wasan gobe duk da cewar har yanzu ya na kan murmurewa daga raunin da ya ji a watan jiya
Ya kuma ce Mbappe ya yi atisaye kamar yadda aka saba a yau, amma gobe ba zai samu damar buga wasan ba, Madrid ce kan gaba a teburin La Liga da maki 49 a wasanni 22, maki daya tsakaninsu da Atletico Madrid wadda zasu hadu ranar Asabar a Santiago, bayan nan kuma zasu ziyarci zakarun Ingila, Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar 11 ga Fabrairu.