Bayan da ƙungiyoyin Real Madrid da takwararta Athletico Madrid su ka buga canjaras a mabanbantan wasannin da su ka buga a gasar Laliga wannan makon, Barcelona na iya ɗare teburin Laliga a wasansu da Vallecano yau.
Barcelona za ta karɓi baƙuncin Rayo Vallecano a filin wasa na Luis Companys da ke birnin Barcelona a wasan mako na 24 na gasar Laliga.
- Ba Za Mu Bari A Yi Wa Olmo Rajista A Barcelona Ba – Javier Tebas
- Barcelona Na Cigaba Da Matsawa Real Madrid Lamba
Maki uku ne a tsakanin Barcelona dake matsayi na uku da Real Madrid dake jan ragamar teburin Laliga,amma kuma damar da Barcelona ke da ita na ɗare wa teburin ita ce yawan ƙwallaye da ta ke dasu a raga.
Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tsallake zuwa matakin zagaye na 16 a gasar zakarun Turai, amma kuma sabon kocin na fatan ganin ya lashe babbar gasar ta ƙasar Sifaniya.