Kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona ta sha kashi a hannun Girona da ci 4-2 a filin wasa na Olymipicos dake birnin Barcelona.
Duk da cewar Lewondowski ne ya fara jefawa Barcelona kwallo a ragar Girona,amma sun farke kwallayen, inda suka jefa kwallaye hudu a ragar Barcelona.
Hakan yasa Girona ta dare matsayi na daya akan teburin La liga, ita kuma Fc Barcelona ta dawo matsayi na hudu.