Barista Aysha Ahmad, kwararriyar lauya ce kuma mai ba da shawarwari ta fuskar Shari’a da harkokin rayuwa, wacce ta tsaya tsayin daka wajen kawo sauyi da karfafa samar da ayyukan dogaro da kai a garinta na haihuwa Zariya da ke Jihar Kaduna. Haifaffiyar garin Zariya ce, birni mai cike da tarihi da al’adu.
Ta yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ta samu digiri a fannin zama kwararriyar lauya (LLB). Daga nan ta samu nasarar shiga makarantar lauyoyi ta Nijeriya tare da cimma nasarori masu dimbin yawa a shekarar 2005.
- Jarin Da Sin Ta Zuba A Bangaren Sufuri Ya Karu A Cikin Watanni 11 Na Farkon 2023
- Amurka Ta Lalata Manufarta Ta Fadin Albarkacin Baki Wajen Watsa Labarai
A kokarinta na fadada neman kwarewa a fannin karatun shari’a, Barr Aysha Ahmad ta wuce zuwa kasar Ingila inda ta samu digirinta na biyu a fannin shari’a a Jami’ar Salford da ke kasar, inda ta karfafa iliminta tare da samun kwarewa a fannonin zamantakewar Duniya.
A daya bangaren kuma, Barr Aysha Ahmad ita ce shugaba kuma mamallakiyar Kamfanin Lauyoyi na Essence Chambers, kamfanin da ya kware wajen tsayawa da wakiltar ‘ya’ya mata da kananan yara Hausa/Fulani a kafatanin Garin Zariya a bangaren shari’a.
Wannan ke kara jaddada sadaukarwarta don warware shinge da tufka da warwara a cikin aikin tabbatar da adalci.
Tasirinta bai tsaya a kotu kadai ba, domin yunkurin da ta yi na kawo sauyi a zamantakewa ya sa ta kafa gidauniyar kula da yara mata ta sarauniya wato (Sarauniya Girls Child Care Foundation).
Wannan gidauniya ta zama hanyar jinkai da share hawaye ga masu karamin karfi a fadin birni da karkara a Nijeriya, ta hanyar samar da sabbin tsare-tsaren yaki da fatara gami da samar da Tallafi.
Aysha Ahmad ta sadaukar da kanta ga inganta rayuwar marasa galihu, musamman ‘yan mata, tare da samar da guraben ayyukan dogaro da kai ya sa ta samu matukar karbuwa sosai a tsakanin al’umma.
Ta kasance mai yawan halartar tarukan kara wa juna sani da manyan tarukan al’umma wanda wannan ya kara haskaka kwarewarta a duniya.
Bayan dimbin yabo da take samu daga ba’arin mutane, ta zama abin koyi ga mutane da yawa masu burin ganin sun kwaikwayi ayyukanta na tausayin al’umma, har ma aka yi mata lakabi da Jagorar Tabbatar da Adalci da Ayyukan Jin kan Al’umma, wato ‘Icon of Justice & Humanitarian Serbices’, Saboda jajircewarta wajen tsayawa kan gaskiya, daidaito, da ci gaban al’umma.