An sako Sarkin garin Okoloke da ke Jihar Kogi, Oba Dada Ogunyanda, bayan ya kwashe kwanaki 27 a hannun waɗanda suka sace shi.
Shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma, Tosin Olokun, ne ya tabbatar da hakan a Lokoja ranar Laraba.
- Yadda Kasar Sin Ta Zo Da Sabon Salon Zamanantar Da Sashen Jigilar Kayayyaki
- An Gudanar Da Taron Ministoci Masu Daidaita Ayyukan Da Aka Amince Yayin Taron FOCAC
Ya ce yanzu Sarkin ya dawo gida yana tare da iyalansa kuma ana yi masa magani.
An sace Oba Ogunyanda, wanda aka fi sani da Obalohun na Okoloke, ne a fadarsa da misalin ƙarfe 2 na dare a ranar 15 ga watan Mayu, 2025.
Shugaban ƙaramar hukumar ya yi jawabi ta bakin mai magana da yawunsa, Sunday Adeyemi, inda ya bayyana godiyarsa ga duk waɗanda suka taimaka wajen dawo da Sarkin cikin ƙoshin lafiya.